Gwamnatin Jahar Katsina ta samu kuɗin shiga Har Naira Biliyan Daya Da Miliyan Ashirin Da Bakwai a watan Takwas na shekarar 2022.

0

A ranar 20/9/2022 aka gudanar da babban taro da ma’aikatar kudi da kasafi ta Jahar Katsina ta shirya a babban dakin Taro na sakatariyar jahar.

Dayake Bayani a wajen taron Kwamishinan Kuɗi na Jahar Alhaji Ƙassim mutallab yace “Gwamnatin jahar katsina ta Samar da Wata Duka ta tattara Kudaden haraji a 2021.

 

Alhaji Ƙassim mutallab Wanda ya samu wakilcin Darektan harkukin mulki na ma’aikatar alhaji muntari lawal.

 

Lawal ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta Gina hedikwatar Hukumar kula da Kudaden haraji a kukarinta na inganta Kudaden shiga da Koma Samar da Kyakykyawan wajen aiki ga ma’aikata da Masu biyan kudin haraji.

 

Lawal ya Kara da Cewa Hukumar ta Samu Babbar na Sara waje Gudanar da Aikace-aikacen na babbatar da tattara Kudaden haraji a jahar.

 

A Cewar Kwamishinan Hukumar ta Samu Nasarar tattara kimanin naira Biliyan Daya Da Miliyan Ashirin Da Bakwai a cikin Shekarar 2022. Ya Kara dacewa Hukumar a shirye take ta Tara Kuɗinda Sukafi haka anan gaba.

See also  Wata Gawa Da Ta Yi Shekara Daya Ana Tunanin Suma Ne

 

kwamishinan kudin yace dolene a hada hannu Domin ganin ansamu Nasarar tattara Kudaden da Suka shafi ma’adanai.

 

Dumin baiwa Gwamnatoci adukkanin matakai damar Gudanar da Aikace-aikacen su Wanda ya kamata, wajen Samar da ababen more rayuwa ga al’ummar su.

A Nashi Jawabin Shugaban tawagar na Shirin kula da tattara Kudaden haraji da kuma Masu hakar ma’adanai na 2022 Alhaji Muhammad Kabir mashi ya yaba ma Gwamnatin jahar akan Babbar tarbar da sukai masu

 

Mashi shine kwamishinan Gwamnatin tarayya na hukumar kula da tattara Kudaden haraji, Kuma Yana wakiltar Jahar Katsina Ya ce wannan Hukumar an kafata ne da manufar kula da yadda Ake rarraba dukkanin arzikin Kasa da kuma yadda Ake tattarasu Zuwa asusun Gwamnati.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here