Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Yajin Aiki Malaman Jami’oi.

0

Kamar yadda muka samu labari daga jaridar The Cable shine cewa kotun masana’antu ta Najeriya (NICN) ta umurci kungiyar malaman jami’a wato ASUU da ta janye yajin aikinta da ke gudana a fadin kasar.

 

Tun a ranar 14 ga watan Fabrairu kungiyar ASUU ta shiga yajin aiki don ganin gwamnatin tarayya ta biya mata bukatunta ciki harda duba albashin malaman jami’a.

 

An yi tattaunawa da dama tsakanin malaman ASUU da gwamnatin tarayya amma duk sai a tashi ba tare da an cimma matsaya ba.

 

Saboda haka, sai gwamnatin tarayya ta garzaya kotu domin kalubalantar yajin aikin.

 

Gwamnati ta hannun lauyanta, James Igwe, ta roki kotu da ta dakatar da ASUU daga daukar wasu matakai dangane da yajin aikin, har zuwa lokacin da za a yanke hukunci kan shari’ar.

See also  Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka

 

Da yake zartar da hukunci a Abuja a ranar Laraba, 21 ga watan Satumba, Justis Polycarp Hamman ya amsa bukatar gwamnatin, jaridar Premium Times ta rahoto.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here