“Idan Katsina Za Ta Iya, Ondo Ma Za Ta Yi’ – Akeredolu Zai Siya Wa Amotekun Bindiga Duk Da FG Bata Yarda Ba.

0

Gwamnan Jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya ce jiharsa za ta siyo wa jami’an hukumar tsaro na yankin yamma, Amotekun makamai, Kamar yadda Jaridar The Cable ta Ruwaito.

 

Babban lauyan mai mukamin SAN ya ce idan gwamnatin tarayya za ta kyalle jami’an tsaro a Katsina su dauki makami, ya kamata a bawa Amotekun wannan damar.

 

“Hana Amotekun damar mallakar makamai na jefa kudu maso yamma cikin hatsari na mahara. Kuma wani mataki ne na lalata bangaren noma a yankin. Barazana ce ga rayuwa.

 

“Muna jadada cewa, ba za mu yarda da fifita wasu jihohi kan wasu ba. Gwamnatin Ondo saboda don sauke nauyin da doka ya dora mata za ta siyo makamai don kare mutanen jihar ta.”

See also  YANZU-YANZU: Gobara ta tashi a kasuwar kayan masarufi ta Singa a Kano

 

Wannan kalaman na Akeredolu na zuwa ne makonni bayan Samuel Ortom, gwamnan jihar Benue, ya ce idan gwamnati ta ki amince wa jami’an tsaron jiharsa su mallaki makamai, zai nemi izini daga mutanensa.

 

Gwamnatin tarayya ta ce hukumomin tsaron da jihohi suka kafa ba su da hurumin mallakar bindiga.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here