Kungiyar hadin-kan al’ummar Musulmai ta duniya wato Rabidatul Alamil Idlamiy wanda take da cibiya a Saudi Arabia ta amince da nadin Sayyadi Ibrahim Sheikh Dahiru Bauchi RA (Khadimul Faidah) a matsayin shugaban Kungiyar a najeriya.
Nadin wanda shugaban ta na Africa Sheikh Khalifa Muhammadu Mahy Niass ya rubuta takarda tare sanya hannu don tabbatar da shi a matsayin wanda zai jagoranci kungiyar a kasar Najeriya. A kwanaki baya ne kungiyar ta nada Sheikh Khalifa Muhammadu Mahy Niass (Khalifan Faidah na duniya) a matsayin shugaban kungiyar na Africa wanda ya samu rakiyan manyan malaman daga kasashen Africa.
Wannan kungiya ta Rabidatul Alamil Idlamiy, kungiya ce wanda take jagoranci dukkanin Musulmai duniya, an kafa tane shekaru fiye da hamsi (50) a kasar Saudi Arabia don warware matsalolin da kasashen Musulmi na duniya ke ciki tare da tallafawa Musulmai duniya ta fannoni da dama.
Sayyadi Alhaji Ibrahim Sheikh Dahiru Bauchi RA shine zai jagoranci kungiyar Rabidatul Alamil Idlamiy ta duniya a najeriya, duk wata kungiya ko akida a najeriya yanzu tana karkashin kulawar shugaban ta na kasa wato Sayyadi Ibrahim Sheikh Dahiru Bauchi RA.
Muna taya Sayyadi Ibrahim Sheikh Dahiru Bauchi RA da samu wannan mukamin, Allah ya taya shi riko, ya tabbatar da alkhairi. Amiin
Majiya: dokin karfe tv