A Yau alhamis 22/9/2022 Babban Sakatare a ma’aikatar ayyuka,Gidaje da sufuri ta jahar katsina Alhaji Bilyaminu Muhammad Albaba yakai ziyarar gani da ido ga ayyukan Gadojin Kasa Dake Kofar Kaura da kofar Kwaya kuma da gadar sama da ake a cikin Birnin Jahar Katsina.
Idandai Ba amantaba a shekarar 2021 Gwamnatin jahar kar Kashin jagorancin Rt. Hon. Aminu Bello Masari ta Kaddamar Da Aikin gina gadar kasa wato (underground) Wacce take a Unguwar Kofar Kaura da kofar Kwaya.
Sana Daga baya aka Kaddamar Da aikin gina babbar gadar sama wato (Fly Over) wacce take a saman Titin tsuhun gidan Gwamnati.