KURFI zata gyara hanyar BIRCHI zuwa WURMA.

0

muazu Hassan

@ katsina city news

Shugaban karamar hukumar kurfi Alhaji Mannir Shehu wurma ya kaddamar da kwamitin da zai duba da tabbatar da kammala aikin gyaran hanyar da ta tashi daga garin Birchi zuwa Lambo ta kuma karasa zuwa wurma.

Hanya ce, mai muhimmaci ga lamarin tsaro da kuma kasuwanci. Gyaran hanyar ba karamin taimaka ma aikin tsaro zai yi ba, da kuma Al ummar yankin.

Idan aka kammala ta, zata iya zama hanyar da jami an tsaro zasu iya bi sukai daukin gaggawa,kurfi,Dutsinma da kuma safana.hanyar Zata amfani duk,kananan hukumomin dake da iyaka da kurfi.

Wadanda aka nada yan kwamitin sune. Shugaba, Injiniya Aliyu Ilyasu wurma daga jami ar Dutsinma, a matsayin shugaba.membonin sune.Dakta Bashir wurma. Muhammad jibrin wurma.sai darakta ayyuka na karamar hukumar kurfi.da shugaban Matasa na garin wurma.sai kansila mai wakiltar yankin Ruma.

See also  Shugaban Sashen Fassara Na Leadership Hausa, Malam Sabo Ahmad Ya Rasu

Aikin an Dora nauyin shi kacokam ga yan yankin yadda in aka samu matsala tasu ce.

Kuma zasu yi aikin da kishi don sun fi kowa sani halin da suke a ciki.

Katsina city news

@ www.katsinacitynews.com

Jaridar taskar labarai

@www.jaridartaskarlabarai.com

The links news

@ www.thelinksnews.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here