Mawaƙiya Jamila Sadi Ta Sake Yin Aure, Shekara 10 Bayan Rabuwarta Da Mawaƙi Sadi Sidi Sharifai

0

FITACCIYAR mawaƙiyar Kannywood, Jamila Usman Alhassan, wadda aka fi sani da Jamila A. Sadi, ta sake yin aure.

 

An ɗaura auren a ranar Lahadi, 18 ga Satumba, 2022 a gidan su da ke unguwar Ƙofar Waika a cikin birnin Kano.

 

Bayan an ɗaura auren, an yi shagalin biki wanda abokan sana’ar ta ‘yan fim da mawaƙa mata su ka halarta.

 

Cikin matan Kannywood da su ka halarci wajen akwai Maryam Saleh (Fantimoti), Maryam A. Baba, Fa’iza Badawa Naja’atu Ta’Annabi, Sadiyar Rarara, Hauwa Edita, da sauran su.

 

Jamila ta yi wannan aure ne bayan ta shafe tsawon shekara 10 tun da ta rabu da tsohon mijin ta, fitaccen mawaƙi Sadi Sidi Sharifai, wanda akwai ƙaruwar haihuwa ɗaya a tsakanin su.

See also  Matar da tayi shekara 40 batayi bacci ba

 

Bayan mutuwar auren nasu, ta dawo Kannywood ta ci gaba da harkokin ta na waƙa.

 

An sha yin hasashen za ta koma ɗakin ta, ana cewa ta na zaman jiran shi Sadin ya amince ya mayar da ita ne, to amma hakan ba ta samu ba.

 

Mu na fatan Allah ya ba da zaman lafiya.

Majiya: Focus news hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here