Za a rage sadaki da kudin biki a China

0

Gwamnatin China ta kaddamar da wani gangami na rage yawan kudin da ake kashewa a yayin biki da kuma rage sadaki Kamar yadda Jaridar daily Nigerian hausa ta Ruwaito

 

Gwamnatin ta yi hakan ne a wani bangare na yunkurin dakatar da raguwar da ake samu a yawan masu aure abin da kuma ya janyo raguwar haihuwa.

 

Kungiyoyi da dama ne suka shiga gangamin, da nufin janyo hankalin mutane a kan rage almubazzaranci yayin biki.

 

Gwamnatin ta ce idan an rage yawan kudin da ake kashewa a lokacin biki za a samu karuwar masu yin aure a kasar.

 

To sai dai kuma masu sharhi sun ce da wuya wannan yunkuri ya yi tasiri, saboda raguwar da al’ummar kasar ke yi ya sa mutane kalilan ne zasu kai shekarun aure.

See also  ASUU ta ki amincewa da tayin N50m daga ordinary president domin kawo karshen yajin aikin.

Majiya: daily Nigerian hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here