Dan Shekara 84 ‘Ya Yi Wa ‘yar shekara takwas Fyade A Ogun

0

‘Yan sanda a jihar Ogun sun kama wani dattijo mai shekaru 84 bisa zargin yi wa wata yarinya ‘yar shekara takwas fyade.

 

Wanda ake zargin, Mai Suna Pa Stephen Jack, wanda ya ke zaune a unguwar Okun Owa a Ijebu Ode, an kama shi ne bayan wani rahoto da aka kai a hedikwatar Obalende.

 

Kakakin rundunar ‘yan sandan, Abimbola Oyeyemi a ranar Asabar ya shaida wa manema labarai a Abeokuta cewa mahaifin yarinyar ya shaida wa ‘yan sanda cewa ya gano ‘yarsa na zubar da jini ta gabanta.

 

A cewarsa, mai karar ya ce lokacin da ya tambayi karamar yarinyar dalilin zubar jinin, sai ta sanar da shi cewa wanda ake zargin ya yi lalata da ita.

See also  ME YA KAI DAMO DA KARE GIDAN GWAMNATIN KATSINA?

 

“Bincike ya nuna cewa dattijon sanannene wajen lalata a yankin,”

 

Oyeyemi ya ce an kai yarinyar zuwa babban asibitin Ijebu Ode domin kula da lafiyarsa.

 

kwamishinan ‘yan sanda, Lanre Bankole, ya bayar da umarnin mika wanda ake zargin zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar domin gudanar da bincike tare da gurfanar da shi gaban kuliya.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here