HUKUMAR HISBAH SUN KAMA MOTAR KUNGIYAR KWADAGO (NLC)

0

A yammacin jiya Juma’a ne Jami’an Hukumar Hisbah da KAROTA dake Kano suka tsallake rijiya da baya bayan wata turka turka da ta barke tsakaninsu da wasu jami’an tsaro akan wata mota da ‘Yan Hisba suke zargi ta dauko Giya zata shigo cikin birnin Kano.

 

Hisbah sun kama wata mota Mai lamabr Kungiyar Kwadago NLC-13-FCT bisa zargin da Giya a ciki Wanda wani Jami’in tsaro yake Mata Rakiya bayan an tsayar da motar sai yaki bada hadin kai Domin bincike harma ya fara harbi a sama, daga Nan sai ga Karin wasu Jami’an Tsaron suka Kori kowa sannan suka umarci Direban ya ja motarashi ya tafi. Isowar shi Na’ibawa sai tayar motar ta fashe inda suka tsaya dan gyarawa.

 

Bayan isowar wasu daga cikin dakarun Hisbah sai wutar ta lafa inda Jami’an Tsaron suka tabbatar da wannan Kaya ba Giya bace Kayan Gwamnati ne Kuma baza a bude ba. Suka nuna Way Bill Mai dauke da tambarin NLC inda yake nuni da fenti da abun Kashe gobara da sauran tarkace suka dauko.

 

Daga karshe an taho Hisbah inda aka bude mota aka ci karo da Barasa (Giya) kala kala a kananan mazubi.

 

Hukumar Hisbah tace zata bi tsarin doka wajen Sauke Kayan Domin ganin abunda ke ciki gaba daya.

 

Ana zargin wasu masu Uwa a Gindin Murhu sun soma zuwa Hisbah Domin ganin an basu Motar.

 

Majiya: Arewa Radio

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here