muazu Hassan
@ katsina city news
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya Amince da baiwa farfesa Sani Abubakar lugga lambar yabo ta girmamawa ta kasa, Mai lambar MFR.
Sakon ya iske farfesa Sani lugga Wazirin katsina na biyar. A wata wasikar da aka rubuto masa a wannan watan na satumba.
Wasikar ta bayyana cewa, za a yi bukin na karrama wadanda aka baiwa lambar ta Girmamawa a ranar 10 ga watan oktoba 2022.
Farfesa sani lugga, Wazirin katsina na biyar, yayi rubuce rubuce da dama wadanda suka bayyana yadda za a warware matsalar kasan nan a fanni daban daban.
Sani lugga kusa ne, a kafa Gidauniyar tallafi ta jahar katsina.( Educational trust funds) da kuma Gidauniyar jahar katsina. ( katsina Foundation)
Shine dan katsina na farko, da ya fara kafa gidan jarida a katsina. Da wata mujalla mai suna News world.
Shine kuma kashin bayan kafa Gidauniyar musulunci.( katsina Islamic foundation) wanda a karkashin ta aka kafa jami ar Musulunci ta farko a Najeriya.
Wazirin katsina na biyar, Uba ne ga kungiyoyin cigaba da yawa a jahar katsina.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com