Yan Bindiga Sun Bindige Wani Dan Kasuwa A Kano A Shagonsa

0

Yan bindiga sun harbe wai dan kasuwa, Mr Ifeanyi, har lahira sun kuma raunata abokinsa a wurin sana’arsa a sabon garin Zaria a Jihar Kano.

 

Daily Trust ta rahoto cewa lamarin ya faru ne a daren ranar Asabar a Azubros Plaza, France Road, Sabon Garin Kano.

 

Shaidu sun ce babu wanda ya san inda yan bindigan suka fito ba har sai da suka ji karar harbin bindiga, suka ce maharan sun bindige mutumin sannan suka tsere a motarsu.

 

Wani shaidan gani da idon, Jibrin Usman ya ce an garzaya da abokin marigayin da aka harba zuwa asibiti yana samun sauki.

 

Duk da cewa kawo yanzu ba a san dalilin kashe shi ba, Daily Trust ta gano cewa marigayin fitaccen dan kasuwa ne da ke sayar da batiri a kasuwan Sabon Gari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here