NDLEA ta Cafke Mai shekara 75 da Zargin Harkar Kwayoyi 

0

Hukumar NDLEA masu yaki da miyagun kwayoyi a Najeriya, tace tayi ram da wani tsoho mai shekara 75 da ake zargi yana harkar kwayoyi.

 

The Guardian tace NDLEA ta bada sanarwar damke wani Usman Bokina Bajama wanda aka fi sai da Clemen a garin Mayo Belwa a jihar Adamawa.

 

Darektan yada labarai da wayar da kan al’umma na NDLEA, Femi Babafemi yake cewa a Talatar makon jiya wannan tsoho ya fado hannun hukumar.

 

Jami’an na NDLEA sun samu Usman Bokina Bajama dauke da kilogiram 49 da ya mallaka daga wata gonarsa da yake shuka taba a Mararraban Tola.

 

Babafemi ya kuma tabbatar da cewa wannan tsoho shi ne kan gaba a jerin mutane 22 da aka yi ram da su bisa zargin mu’amala da mugayen kwayoyi.

 

Kamar yadda Kakakin hukumar ya fada, an yi nasarar karbe fiye da kwalabe miliyan daya (1,001,387) na Akuskura da aka haramta yin amfani da shi.

 

Jaridar Tribune tace baya ga maganin Akuskura da kuma tramadol da aka samu, jami’an NDLEA sun karbe kilogiram 2, 536 na tabar wiwi a jihohi.

 

A jawabinsa, Babafemi yace an lalata eka goma na miyagun kwayoyi da aka shuka a gonaki. NDLEA tayi wannan aiki ne a garuruwan Edo da Adamawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here