GWAMNA MASARI YAYI KIRA GA KAMFANIN KEDCO DA SU RAGE KUDIN WUTA 

0

Mai girma Gwamnan jihar Katsina, Rt. Hon. Aminu Bello Masari ya nuna damuwar sa dangane da tsawwalla wa al’umma da kamfanin rarraba wutar lantarki na kedco ke yi wa jamaar jihar katsina .

 

Gwamnan ya yi koken ne lokacin da yake jawabi yayin da ya karbi bakuncin sabon manajan Daraktan kamfanin Alh Ahmad Dangana Wanda ya kawo wa gwamnan ziyara a Gidan Muhammadu Buhari fadar Gwamnatin jihar katsina.

 

Haka kuma Dallatun katsina ya nuna damuwar sa kan irin yanda kamfanin ke Kara kudin wutar ba Kai ba gindi, ya Bayar da misali da abinda ya faru na Karin kudin wutar cibiyoyin gwamnatin jihar katsina, daga naira Miliyan 36 a wata zuwa naira Miliyan 70.

 

Daga nan sai ya ja hankalin sabon manajan Daraktan da yayi wani abu domin saukaka wa al’umma .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here