Gwamnatin tarayya za ta karrama malamin makarantar FGC Birnin-Yawuri wanda a lokacin da yan ta’adda suka kwashe daliban makarantar ya ce shi ma su tafi da shi domin a matsayinsa na uba ba zai iya jure a wuce da ya’yansa a barshi ba.
Gwamnatin tarayyar zata karrama Malam Mukhtar Gulma ne da lambar girmamawa ta kasa wato Member of the Order of Niger (MON).
Sanarwar hakan ta fito ne a cikin wata takarda da Ministan ayyuka na musamman wato Special Duties Sanata George Akume ya sanyawa hannu kuma aka aika masa.
Taron karramawar zai gudana ne a ranar talata 11/10/2022 a dakin taro na International Conference Center dake Birnin Tarayya Abuja.