Matar Da Ta Haifi Ƴan Biyar Tana Samun Kulawa Da Jaririnta A Asibitin Koyarwa Ta Gwamnatin Tarayya Dake Katsina

0

Malama Hajara Shuaibu, Yar Asalin Karamar Hukumar Faskari A Jihar Katsina Ta Haifi Ƴan Biyar Reras A Ranar Laraba Da Ta Gabata, Inda Ta Haifi Maza Ukku Da Mata Biyu.

 

Majiyar RARIYA Ta Nakalto Cewa Malama Hajara Ta Haife Su A Gidanta, Daga Baya Kuma Aka Kaita Babbar Asibitin Karamar Hukumar Funtua Daga Nan Aka Turo Su Asibitin Koyarwa Ta Gwamnatin Tarayya Dake Katsina Domin Samun Kulawa Da Jaririnta.

 

Haka Zalika, Majiyar Ta Shaida Mata Cewa Ɗaya Daga Cikin Jaririn Namiji Da Mace Guda Allah Ya Yi Masu Rasuwa, Sauran Ukku Suna Samun Kulawa Kuma Suna Kara Murmurewa A Waje Na Musamman Da Ake Kula Da Jarirai Na Asibitin.

 

majiya: rariya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here