‘Yan ta’adda sun kashe Mutane biyu, sun yi garkuwa da mutun uku a Katsina

0

Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a ranar Lahadin, sun bude wuta kan wasu mazauna Katsina, inda suka kashe mutum biyu tare da yin garkuwa da wasu uku.

 

Wani mazaunin yankin da ya koka kan lamarin, Malam Yusufu Musa, ya ce ‘yan bindigar na kai farmaki ne daga dajin da ke karamar hukumar Jibiya a jihar Katsina.

 

DAILY POST ta Ruwaito  wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne a kwanakin baya, sun kai hari tare da yin garkuwa da wani dan kasuwa a unguwar guda. An kashe shi ne duk da naira miliyan hudu da aka biya kudin fansa a karamar hukumar Kafur.

 

Sai dai rundunar hadin guiwar sojojin Najeriya da ‘yan sanda sun kasa kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su duk da cewa sun yi artabu da ‘yan ta’addan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here