An Kama Wani Mai Unguwa Da Laifin Hada Baki Da Yan Ta’adda A Jahar Katsina

0

Daga Muhammad kabir

Rundunar yan sandan jahar katsina karkashin jagorancin cp shehu umar nadada ta samu na sarar kama wani mai unguwa a wani kauye Mai suna gobirawa a cikin karamar hukumar faskari ake a jahar.

Da yake magana da manema labarai, kakakin rundunar SP Gambo Isah yace a ranar 19 ga watan Oktoba na Shekara 2022, An kai wa wani mai suna Yahaya Danbai, ɗan shekara 35 hari a gonarsa da bindiga.

“Manomin sai allah ya bashi na nasara, ya yi galaba a kan Dan ta’addan, ya kwace makamin da ke hannunsa ya kuma kashe ɗan ta’addan.

“Ya dauki bindigar da ya kwace ya kai ta gidan Mai Unguwa Mai Suna, Malam Surajo. Yayi ma Mai Unguwa Bayani.

“Amma Malam Surajo Mai makon ya ɗauki wannan Bindiga ya Kaima Yan Sanda, A’a sai ya kirawo wani Dan ta’adda Mai Suna Hamisu.

“To dama ya kulle shi wannan manomi a gidan sa. Hamisu da yazu yaga wannan gawar, ya Shaida yaron sane aka Kashe, sai Mai Unguwar ya damka Masu wannan manomi sai Suka halbe shi har lahira. Sana sai Mai Unguwar ya Basu bindigar su.

“Sai Yan Bindiga Suka shigo gari Suka ce tunda an kashe Masu Dan Uwa to sai an biya kudin diyya har naira miliyan 10, Idan ba hakaba to Zasu shigo Garin su Kashe kuwa.

SP Gambo Isah ya Kara da Cewa “Rundunar Yan Sanda sunsamu Labarai afkuwar Lamarin sai Mai Unguwar ya gudu ya buya, amma daga bisani sai ya shigo hannu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here