An kama wani mutune da yake saka kayan mata don damfarar mutane a Adamawa

0

Wani mutum a jihar Adamawa ya gurfana a gaban kotu da laifin sanya tufafin mata don yaudarar maza gami da amshe kudaden su.

Mutumin, mai suna Muhammed Abubakar, ya ce ya saba sanya kayan mata tare da fita da abokansa mata domin samun kudi a wajen maza masu bukatar soyayya.

Muhammed wanda ke da Diploma a fannin kasuwanci daga Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Adamawa, ya ce matan da suke fita aiki suna ba shi tsakanin Naira 500 zuwa N1,500 a kullum a matsayin kason sa na ganima.

Muhammed ya shaida wa babbar kotun majistare da ke Girei inda aka gurfanar da shi a gaban kotu, cewa matan da yake tare dasu Suna kareshi a duk lokacin da wani mutum ya so ya same shi, ta hanyar gaya wa mutumin cewa ita (shi) tana cikin hailar.

An ranar 22 ga watan Nuwamba, 2022, wasan Muhammed ya kare, ya shiga kasuwar Girei inda ya je sayan dan kunne sai wani mutum ya gan shi wanda ya yi zargin cewa wannan na mijine.

Kotun karkashin jagorancin Martina Gregory kuma ta ba da umarnin a tsare shi har zuwa ranar 5 ga Disamba, 2022.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here