Yan bindiga sun nemi sabuwar Naira a matsayin kudin fansa bayan sun yi garkuwa da mutanen kauyuka a Zamfara

0

Wasu ‘yan bindiga sun bukaci a ba su sabbin kudi na naira a matsayin kudin fansa bayan sun yi garkuwa da akalla mutane hudu a kauyen Kolo da ke karamar hukumar Gusau a jihar Zamfara.

Intelregion ta ruwaito cewa barayin sun nemi kudin fansa N10m domin su sako wadanda lamarin ya rutsa da su da suka hada da namiji, mace da yara biyu sun ki amincewa da tsohuwar takardar naira.

Wani dan asalin yankin mai suna Mohammed Ibrahim, ya ce daga baya ‘yan fashin sun rage kudin fansa zuwa N5m, inda ya ce mutanen kauyen sun yi ta kokarin tara kudin domin a sako wadanda lamarin ya shafa.

“A yayin da muke kokarin tattara kudaden da ‘yan ta’addan suka nema, sun sake aika da wani sako da safiyar yau cewa ba za su karbi tsoffin takardun naira ba.

“Sun ce za su ci gaba da ajiye wadanda suka sace a sansanonin su har sai an fitar da sabbin takardun Naira a watan Disamba,” in ji Ibrahim.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here