Ɓeraye sun shanye hodar ibilis ɗin da ƴan sanda su ka ƙwace su ka ajiye a Caji-ofis

0

Yan sanda a Indiya sun ce ɓeraye sun lalata kusan kilogram 200 na hodar ibilis da aka ƙwace a hannun wasu mutane da ke safararta aka kuma ajiye a ofishinsu.

 

“Ɓeraye kananan halittu ne da ba su san wani tsoron ‘yan sanda ba. Abu ne mai wahala iya kare su,” a cewar Kotu da ke zamanta a jihar Uttar Pradesh.

 

BBC ta rawaito cewa kotun ta bukaci ‘yan sanda su gabatar da shaida da ke tabbatar da cewa ɓeraye ne suka lalata hodar.

 

Alkalin ya bada misali da kararraki uku da aka gabatar kan ɓeraye sun lalata kwayar.

 

Mai shari’a Sanjay Chaudhary ya ce ko a baya an samu rahotanni da ke cewa ɓerayen sun lalata kilo 195 na hodar iblis, da kuma kilo 700 duk a ofisoshin ‘yan sanda.

See also  Masu Aikin Shara Sun Ci Naira Tiriliyan Daya A wajen Caca

 

Sanjay ya faɗawa ‘yan sanda cewa ba su da kwarewar yaƙi da irin waɗannan ɓeraye. Ya ce hanya ɗaya tilo na kare aukuwar irin wannan shi ne kai hodar ko kwayar dakunan adana magunguna ko aiwatar da gwaji.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here