Gwamnatin jihar Kano ta fara shirin gyara makarantu 21 a fadin jihar.

0

Manajan Daraktan na Hukumar Tsare-Tsare da Cigaban Birane ta Jihar Kano, KNUPDA, Suleiman Abdulwahab ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis a lokacin da ya kai ziyarar duba wasu makarantun da ake gyarawa a cikin babban birnin.

malam Suleiman ya ce an dauki matakin ne domin ganin an gudanar da koyo da koyarwa cikin yanayi mai kyau.

Suleiman ya ce “Wannan ya kara jaddada manufar gwamnatin jihar na fitar da kayan aiki masu inganci a fadin makarantu mallakar jihar ta hanyar samar da ababen more rayuwa masu muhimmanci don saukaka ingantaccen koyo da koyarwa.

“Muna fatan ganin karin PPPs a fannin ilimi tare da tagwayen manufar inganta kayayyakin more rayuwa da inganci tare da rage nauyin bayar da kudade a fannin da samar da tsaro ga makarantu.

“A karkashin wannan aikin, an zabo makarantun gwamnati guda 21 a cikin shirin gwaji a cikin babban birni a matsayin wani mataki na magance matsalar rashin tsaro da yawancin makarantun ke fuskanta sakamakon ayyukan bata gari da kuma hanyoyin samun kudin shiga ga mahukuntan makarantun domin kula da su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here