Hukumar NDLEA ta kama tan 1.5 na haramtattun kwayoyi, ta kuma kama mutane 993 a Katsina.

0

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta kame tan 1.5 na miyagun kwayoyi tare da kama wadanda ake zargi 993 a jihar Katsina daga ranar 10 zuwa 23 ga watan Nuwamba.

Kwamandan NDLEA a jihar, Muhammad Bashir ne ya bayyana hakan ga manema labarai kan ayyukan hukumar.

Da yake jawabi, ya bayyana lokacin da ya karbi ragamar tafiyar da hukumar a jihar a matsayinsa na kwamanda na 16 da aka tura jihar.

Kwamandan ya kuma bayyana cewa, akasarin wadanda aka kaman basu wuce shekaru 16 zuwa 40 ba

Bashir ya kuma bayyana cewa, wani sashe na hukumar ya yi nasarar gyara haliyen mutune 76 daga kawo shi.

Daga karshe ya yabawa gwamna Masari da irin kokarin da yake da kuma tallafawa hukumar da yake a kowane lokaci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here