Kotun daukaka kara ta dawo da Aisha Binani a matsayin ‘yar takarar gwamna a jam’iyyar APC a Adamawa

0

Kotun daukaka kara da ke zamanta a Yola ta mayar da Sanata Aishatu Ahmed Binani a matsayin ‘yar takarar gwamnan jihar Adamawa a karkashin jam’iyyar APC.

 

Hukuncin guda uku da babban alkalin kotun Tani Yusuf Hassan ya karanta a ranar Alhamis, 24 ga watan Nuwamba, 2022, ya yi watsi da hukuncin da babbar kotun tarayya da ke Yola ta yanke, wadda ta kori Binani.

 

Don haka kotun daukaka kara ta umarci jam’iyyar APC da ta sake mika sunan Binani ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) a matsayin yar takarar gwamna.

 

Idan zaku tuna cewa a ranar 14 ga Oktoba, 2022, wata babbar kotun tarayya da ke Yola ta soke zaben fidda gwani na gwamna na jam’iyyar APC wanda ya samar da Binani a matsayin yar takarar gwamna na jam’iyyar.

 

Mai shari’a Abdul-aziz Anka ya soke zaben da aka yi ma Binani, Don haka ya bayyana cewa APC ba za ta iya tsayar da kowane dan takara a zaben 2023 ba.

 

Sai dai alkalin kotun daukaka kara, Hassan ya bayyana cewa karar da aka shigar ta hanyar sammacin ta taho ne zuwa kotun daukaka kara da batutuwa takwas domin tantancewa, tare da tambayoyi biyu.

 

Don haka ta bayyana cewa biyar daga cikin takwas an yi watsi da su yayin da sauran ukun aka warware su a madadin mai kara (Binani).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here