Mahaifiyarta Ta Nemi Na Yi Wa Budurwata Ciki Ni Kuma Na Aikata, 

0

Wani matashi mai suna Sadiq ya faɗa wa wata Kotu a Ibadan babban birnin jihar Oyo, cewa mahaifiyar budurwarsa ce ta nemi ya ɗirka wa ɗiyarta ciki kafin a ɗaura musu aure.

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa Sadiq ya bayyana wa Kotu komai ne yayin da yake kokarin kare kansa a zaman Shari’ar da budurwar ta kai shi ƙara.

Budurwar, wacce ta riga ta haife cikin, ta kai ƙarar Sadiq ne bisa zargin baya bata kulawar da ya kamata.

Da yake wa Alƙali jawabi a zaman Kotun, wanda ake zargi yace ya aikata abinda iyayen budurwarsa suka nema a wurinsa amma daga baya kuma suka juya masa baya.

Sadiq yace “Ban san wace matsala ce ta faru ba, iyayen yarinyar suka same ni suka gaya mun cewa sam ba zasu amince ɗiyarsu ta zauna zaman aure da ni ba. Kuma an hana ni ganin ɗan da ta haifa mun.”

Tun da farko mai shigar ƙara ta gaya wa Alkalin Kotun cewa Saurayin ya watsar da ita, ba ya bata kulawa da ɗanta da suka haifa mai shekara uku.

Alkalin Kotun mai shari’a Misis S.M. Akintayo Ta yanke hukuncin cewa yaron ya zauna a wurin mahaifiyarsa yayin da shi kuma Sadiq zai rinƙa baiwa budurwar N10,000 a kowane wata

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here