Dan takaran kujerar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa ko shakka babu zai lashe zaben jihar Anambra a 2023.
Wannan shine jawabinsa yayin zaman hada kan kungiyoyin magoya bayansa sama da guda 200 dake jihar karkashin jagorancin Dirakta Janar na kamfen Atiku-Okowa na jihar, Farfesa Obiora Okonkwo.
Okonkwo ya bayyana cewa ko shakka babu Atiku Abubakar da Ifeanyichukwu Okowa, zasu baiwa Peter Obi mamaki a watan Febrairun na 2023,