‘Yan jam’iyyar APC na Kano suna son a hukunta Bashir Ahmad saboda barin jam’iyyar ya tafi kallon buga a gasar cin kofin duniya a Qatar

0

Wasu ‘ya’yan jam’iyyar All Progressives Congress, APC, a Kano sun bukaci shugabannin jam’iyyar da su gaggauta daukar tsauraran matakai kan mai taimaka wa shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad, bisa zarginsa da rashin mutunta ci gaban jam’iyyar.

 

Mambobin sun zargi Bashir Ahmad da halartar wasan karshe na gasar cin kofin duniya da ake yi a kasar Qatar.

 

Alhaji Samani Inuwa, daya daga cikin shugabannin jam’iyyar daga karamar hukumar Gaya, ya shaidawa manema labarai tare da wasu mambobin kungiyar cewa lamarin Ahmad ya jawo damuwa.

 

Ya ce, “ba za mu iya fahimtar yadda Bashir Ahmad ya zabi zama a Qatar a lokacin da muke Kano muna karamar hukumar Gaya domin kaddamar da yakin neman zaben gwamna da sauran mukamai na jam’iyyar.

 

“Idan kowane dan jam’iyyar zai yi irin yadda Bashir ya aikata, ba ma tunanin APC za ta kai ga ofishin zabe, don haka ya kamata a gaggauta hukunta shi don ya zama Aya ga wasu.”

 

Haka zalika shugabannin jam’iyyar sun taya gwamna Abdullahi Ganduje murnar ganin an gudanar da yakin neman zaben gwamna a garin Gaya cikin kwanciyar hankali.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here