ZARGIN DAMFARA: ‘Ka koma Kotun Tarayya ka fuskanci tuhumar – Umarnin Kotun Ƙoli ga ɗan takarar sanatan Kano, AA Zaura

0

Kotun Ƙoli ta umarci ɗan takarar Sanatan Kano ta Tsakiya, Abdulsalam Abdulkarim cewa ya koma Babbar Kotun Tarayya ta Kano ya fuskanci tuhumar damfarar da ake yi masa.

 

Abdulkarim wanda aka fi sani da AA Zaura, ya shiga tsomomuwa tun cikin 2018, yayin da EFCC ta gurfanar da shi Babbar Kotun Tarayya da ke Kano, inda aka tuhume shi da laifin damfarar wani Balaraben Kuwaiti dala miliyan 1.3.

 

Sai dai kuma a ranar 9 Ga Yuni, 2020, Mai Shari’a Lewis Allagoa na Kotun Tarayya, Kano, ya sallame shi, bisa dalilin cewa EFCC ta kasa gabatar da cikakkiyar hujjar cewa AA Zaura ya damfari Balaraben mai suna Jamman Al-Azmi maƙudan dalolin.

 

Mai Shari’a ya ce EFCC ta kasa gabatar da wanda aka ce anfara a kotu, domin ya yi bayanin yadda aka damfare shi.

 

Bayan yanke hukunci, EFCC ta ƙi amincewa da hukuncin, inda ta garzaya Kotun Ɗauka Ƙara.

 

Alƙalai uku a Kotun Ɗaukaka Ƙara sun yi nazarin hukuncin da Mai Shari’a na Kotun Tarayya, Allagoa ya yanke, inda jagoran su ya ce tilas Zaura ya fuskanci hukunci.

 

Daga nan sai jagoran Alƙalan uku, Abdullahi Bayero, ya bada umarnin a maida shari’ar hannun wani mai shari’a daban, ba Allagoa ba.

 

Maimakon AA Zaura ya haƙura ya koma ya fuskanci tuhuma, sai ya garzaya Kotun Ƙoli.

 

Sai dai a can ma bai yi nasara ba, inda yanzu bayan Alƙalan Kotun Ƙoli sun yi nazarin yadda lamarin ya ke, jagoran su Inyang Okoro ya ce, “Kotun Ƙoli ba ta da hurumin hana Kotun Ɗaukaka Ƙara tuhumar AA Zaura, domin abin da ake zargin ya yi laifi ne da ya shafi laifi na manyan maɓarnata.

 

Daga nan Kotun Ƙoli ta ce AA Zaura ya koma ya fuskanci tuhuma a Babbar Kotun Tarayya, ƙarƙashin wani Mai Shari’a, ba na farkon da ya wanke shi ba.

 

An dai umarci AA Zaura ya bayyana a gaban kotu, a ranar 5 Ga Disamba.

 

Ana zargin sa da damfarar Balarabe dala miliyan 1.3, wadda ya karɓa tun cikin 2018, ya ce zai sai masa kadarori a Dubai da Kuwait, amma shiru ka ke ji.

 

AAA Zaura dai ya yi takarar gwamnan jihar Kano a 2019, ƙarƙashin GPN.

Majiya: premium times hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here