Bayan Uwargidar Shugaban Kasa Ta Yafe Masa, Aminu Zai Gana Da Buhari A Villa Yau 

0

Matashin Nan Dan jihar Jigawan da yaci mutuncin Hajiya Aisha Buhari, uwargidar shugaban kasa, Mai Suna Aminu Mohammed Adamu, ya samu yanci. Bayan Uwargidar Shugaban Kasa Ta Yafe Masa.

 

Aminu wanda tuni an sakeshi daga kurkukun Suleja zai gana da mijin Aisha, Shugaba buhari kafin ya koma wajen iyayensa, Inji Jaridar Leadership.

 

Wanda ke matsayin Uba ga Aminu, Malam Kabiru Shehu, shi ya bayyana hakan. Shehu ya ce Aminu yanzu haka yana Aso Villa kuma yana shirin ganawa da Shugaba Buhari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here