‘Yan ta’adda sun harbe limami, sun yi awon gaba da masallata 13 a Katsina

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina a ranar Lahadi ta tabbatar da ceto wasu mutane shida da ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su a daren ranar Asabar a karamar hukumar Funtua da ke jihar. Kamar yadda Jaridar punch ta ruwaito.

Mutanen 6 da lamarin ya rutsa da su na daga cikin masallata 19 da ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su da misalin karfe 7:40 na yammacin ranar Asabar a wani masallaci da ke unguwar Maigamji a karamar hukumar Funtua.

Mutanen 19 suna sallar magariba ne a cikin masallacin, sai ‘yan ta’addan suka far musu suka yi awon gaba da su cikin dajin a daren.

Mazauna yankin sun ce ‘yan ta’addan sun harbe babban Limamin da ke jagorantar sallar tare da raunata wani mai ibada a yayin harin kafin su yi awon gaba da mutanen.

An kuma bayyana cewa, da farko tawagar ‘yan sanda da ‘yan banga sun ceto biyu daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su a daren ranar Asabar yayin da aka ceto sauran hudun da sanyin safiyar Lahadi.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Gambo Isah, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce, “Gaskiya ne harin ya faru. ‘Yan ta’addan sun mamaye masallacin da ke Maigamji ne a daidai lokacin da jama’a ke gudanar da Sallar Isha’i. Sun harbe Imam da kuma wani mutum guda. Wadannan mutane a halin yanzu suna karbar magani a asibiti. ‘Yan ta’addan sun kuma yi awon gaba da wasu masu ibada a cikin daren, amma hadin gwiwar ‘yan sanda da ‘yan banga sun ceto biyu daga cikin wadanda abin ya shafa a daren. Jami’an tsaron sun kuma ceto wasu mutane hudu da suka mutu a ranar Lahadin da ta gabata, wanda ya zuwa yanzu an ceto jimillar mutane shida.

“Yanzu haka mutane 13 da abin ya rutsa da su na hannun ‘yan ta’addan kuma jami’an mu suna bakin kokarinsu wajen ganin an ceto su ba tare da wani rauni ba.

Mazauna yankin da aka zanta da su ta wayar tarho a ranar Lahadin da ta gabata sun ce al’amura sun lafa duk da cewa har yanzu da yawa na cikin damuwa kan lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here