Fitacciyar jarumar masana’antar shirya fina-finan Kannywood da Nollywood, Rahama Sadau, ta cika shekaru 29 a duniya, a yau Laraba, 7 ga watan Disamba.
Domin raya wannan rana, Rahama ta saki wasu zafafan hotunanta a shafinta na Instagram tana mai nuna farin ciki tsanta.
Jarumar ta kuma yi godiya ga Allah Ubangji da ya nuna mata wannan rana a raye kuma cikin koshin lafiya da annashuwa.
“SHAFI NA 29 ♂️
“Murna da zagayowar ranar haihuwata, “Rahama yarinya mai kaunar kanta, karfi, kyau da ban mamaki❤️
“Akwai abubuwan godiya da dama, amma babu wanda ya fi kasancewa a raye, cikin koshin lafiya da farin ciki.
“Alhamdulillah ga wata shekara mai albarka. “Ya Allah, Nagode da ni’imar da kayi mani ❤️♂️.”