Wani Jigo a Jam’iyyar APC yace Babu Wanda ya Isa ya kadasu a jahar Shugaban Kasa.

0

Ministan harkokin jirgin sama, Hadi Sirika yana ganin cewa babu wanda ya isa ya gwabje jam’iyyar APC mai mulki a babban zabe mai zuwa. A wani bidiyo da Gwagware Reporters suka fitar kwanan nan, an ji yadda Sanata Hadi Sirika yake cika baki da cewa APC ta tanadi kudin yakin zabe.

Hadi Sirika ya yi wannan jawabi ne a wajen bikin da aka shirya domin tarawa Dr. Umar Dikko Radda kudin kamfe.

An shirya taro na musamman a birnin tarayya Abuja da nufin karbar gudumuwar magoya baya wajen yakin neman zaben Dikko/Jobe a jihar Katsina.

Da ya tashi jawabi, Sirika wanda Minista ne a gwamnatin Muhammadu Buhari tun karshen 2015, yace ba za ta yiwu ‘yan adawa suyi galaba a kansu ba.

Dan siyasar ya kuma cika-baki da cewa jam’iyyun hamayya ba za su iya galaba a kan Gwamna Aminu Bello Masari a karamar hukumar Kafur ba.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here