Wasu ‘yan bindiga sun sace basaraken gargajiya mai daraja ta daya a Jos

0

Wasu ‘yan bindiga da har yanzu ba a san ko su wanene ba sun yi garkuwa da wani basarake mai daraja ta daya a jihar Filato, Agwom Izere, Mai Martaba Dokta Isaac Azi Wakili.

Rahotanni sun ce an yi garkuwa da Sarkin ne a safiyar ranar Juma’a a Fadarsa da ke gundumar Shere ta Gabas ta Jos inda aka kai shi wani wuri da ba a sani ba.

Maharan sun kutsa kai cikin fadar inda suka yi ta harbin jami’an tsaron da ke fadar.

Jami’an tsaro biyu sun samu raunuka iri-iri ko da ‘yan bindigar sun mamaye su tare da tafiya da basaraken.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Alfred Alabo, ya bayyana cewa an tura wata tawaga ta dabara zuwa yankin Izere domin ceto wadanda aka yi garkuwa da su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here