JAMA’AR GARI DA JAMI’AN TSARO SUN FAFATA DA YAN BINDIGA A GARAN DAN GARU

0

musbahu Ahmad Batsari

@ katsina city news

A ranar juma’a 20-01-22023, da misalin ƙarfe tara (09:00am) na safe wasu ƴan bindiga suka afka ma ƙauyen Ɗan-garu dake cikin yankin ƙaramar hukumar Batsari ta jihar Katsina, inda suka yi ta ɗauki ba daɗi da mutanen ƙauyen har Allah ya basu nasarar kashe ƴan bindiga biyu, sannan aka harbi mutum ɗaya cikin mutanen garin.

Bayan ƙura ta lafa da la’asar misalin ƙarfe huɗu na yamma suka sake yo gangami suka yi ma ƙauyen ƙawanya da nufin ɗaukar fansa inda ƴan bindiga suka kashe mutane tara daga cikin mutanen ƙauyen, amma majiyar mu ta bayyana cewa jami’an tsaro sun kai ɗauki har samu nasarar kashe da dama daga cikin ƴan bindigar. kamar yadda aka labarta mana har jirgin yaƙi yakai ɗauki kuma ya jefa masu bama-bamai lokacin da suka fita wajen garin suna ƙoƙarin tserewa.

@ katsina city news

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here