fusatattun matasa a Kano sun jefi ayarin motocin Shugaba Buhari da jirgin sa mai saukar ungulu.

0

Fusatattun matasa a jahar Kano sun fito kwansu da kwarkwata domin nuna adawa da ziyarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai na kaddamar da ayyukan gwamnatin tarayya a jihar.

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan wani abu makamancin haka ya faru a Katsina, mahaifar shugaban kasar.

Watakila zanga-zangar ba ta rasa nasaba da irin wahalhalun da ‘yan Najeriya ke fuskanta a halin yanzu sakamakon tsadar farashin man fetur da karancin man fetur da kuma sake fasalin kudin Naira.

Fusatattun matasan wadanda suka kunna wuta a kan hanyar Maiduguri a jahar tare da rera wakokin ba ma yi, sun rika jifan ayarin motocin da duwatsu daga nesa duk da jami’an tsaro da hayaki mai sa hawaye da akasaki.

Jaridar daily nigerian ta ruwaito cewa an rufe wasu sassa na dukkan manyan tituna hudu hadda gadar Muhammadu Buhari da aka gina na tsawon kwanaki biyu ana jiran ziyarar shugaban.

A cikin faifan bidiyon da ya karade shafukan sada zumunta, an ga wasu matasa suna jifan jirgin saman shugaban kasa a lokacin da ya tashi bayan kaddamar da manyan ayyukan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here