INA NAN A NNPP TAKARAR MATAIMAKIN GWAMNA.NA BARI  ….inji Muttaqa Rabe Darma 

0

Injiniya Muttaqa Rabe Darma ya tabbatar ma da jaridun katsina city news cewa yana nan a matsayin sa na Dan jam iyyar NNPP amma takarar mataimakin gwamna ce ya ajiye .

Muttaqa ya fadi hakan ne a wata waya da ya buga ma babban editan jaridun katsina city news.

A sakon wayar ya bayyana cewa ya San yadda ake barin jam iyya don haka babu daya da aikata na barin jam iyyar NNPP

Muttaqa ya tabbatar ma da jaridun cewa ya rubuta ma hukumar INEC cewa ya bar takarar sa ta mataimakin gwamna.

Injiniya Muttaqa Rabe yace har yanzu shi halastaccen Dan jam iyyar NNPP ce .

Jaridun katsina city sun samu labarin su ta Majiya daga hukumar INEC da kuma sakataren jam iyyar NNPP da suka tattauna dashi

Kafin rubuta labarin sunyi magana da injiniya Muttaqa Rabe Wanda a lokacin yaki magana yace sai dai a tuntubi jam iyya ko kuma Dan takarar gwamna injiniya Nura Khalil

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here