Gamayyar Kungiyoyi A Katsina Masu Suna (Coalition Of Katsina Group For National Unity & Integration) Sun Kalubalanci Atiku Abubakar 

0

Daga Muhammad Kabir

An Kalubalanci Ɗan Takarar shugabancin ƙasa Alhaji Atiku Abubakar akan Wasu maganganu nasa da yayi.

Hakan dai na kunshe ne a yayin ganawa da manema labarai da ƙungiyar ta kira ranar Juma’a 3/2/2023 a Babban Dakin taro na Kungiyar Yan jaridu ta NUJ reshen jahar Katsina.

Shugaban Kungiyar Hamza Umar Saulawa yace “Kamar Dan Takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar wai Yayi kira ga Gwamnatin Tarayya wai kada a Kara Lokaci. hakan na nuna cewa Atiku Abubakar baya tausayin Talakan Najeriya.

“Batu na biyu kuma shine mungani a jaridar daily trust, Shugaban yakin Neman Zaɓen Atiku ya fito Karara yace Idan Atiku Abubakar ya zama Shugaban Kasa Zai saki Nnamdi Kanu, Ba tare da anyi shari’a akan shiba.

“Waɗannan Maganganu ba Zasuyi ma Yan Arewa dadiba haka Kuna ba Zasu Kawo hadin Kai ba a Kasa, haka zalika duk Wani Mai Kishin Kasa ba Zaiyi masa dadiba.

Hamza Umar Saulawa ya Kara da cewa Dalilin siyasa ace Za’a saki Mutumin da yayi sanadiyyar mutuwar Yan Arewa Masu Neman abinci a Ƙasarnan da Jami’an Tsaro da Sojoji.

Dalilin siyasa ace Za’a saki Mutumin da yayi sanadiyyar mutuwar ma aikatan zaɓe a Kudancin kasar waɗanda basa kilguwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here