‘Yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutane 41 a Katsina

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da mutuwar ‘yan banga 41 da aka fi sani da ‘Yansakai’ a wani harin kwantan bauna da ‘yan ta’adda suka kai a dajin Yargoje.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, SP Gambo Isah, ya raba wa manema labarai ranar Juma’a a Katsina.

“A ranar Laraba, 1 ga watan Fabrairu, 2023, da misalin karfe 22:00, ‘yan ta’addan suna harbe-harbe da bindigogi kirar AK 47, sun kai hari gidan wani Alhaji Muntari da ke Unguwar Audu Gare, Kandarawa, karamar hukumar Bakori, tare da yin awon gaba da shanu da tumaki 30.

“Daga baya, a ranar 2 ga Fabrairu, da misalin karfe 10:00, kungiyoyin Yansakai daga kauyuka 11 na karamar hukumar Bakori suka sake haduwa suka bi ‘yan ta’addan da nufin kwato dabbobin da suka sace.

“Sun bi hanyar ‘yan ta’addan zuwa wani wuri a dajin Yargoje, abin takaici, ‘yan ta’addan sun shirya tare da kai harin kwantan bauna a Yansakai.

“Yan bindigar sun harbe Yansakai 41 tare da raunata wasu biyu,” in ji shi.

Isah ya ce, Kwamandan yankin na Malumfashi ya shigo manyan ‘yan sanda zuwa wurin da lamarin ya faru, inda suka kwashe gawarwakin da wadanda suka jikkata zuwa babban asibitin Kankara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here