
Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta kama wani mutum mai suna Abdulrahman Woru dan shekara 38 da ake zargi da aikata tsafi da kokon kan mutum a garin Babana da ke karamar hukumar Borgu ta jihar.
Wanda ake zargin wanda ke zaune a Babana, dan kauyen Gbesewona ne na Jamhuriyar Benin.
Rundunar ‘yan sandan ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, DSP Wasiu Abiodun, ya sanyawa hannu a Minna.
Ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar 24 ga watan Junairu 2023 bisa ga wani rahoto da aka samu.
Ya bayyana cewa an kama wanda ake zargin ne a Babana bayan da ake zarginsa da wani kokon kan mutum.
A cewarsa, “a lokacin da aka gudanar da bincike a gidansa, an gano wani kwanyar mutum, wasu guda uku da ake zargin hakarkarin mutane ne gumaka biyu da tsabar kudi CFA 5000 na kudin Jamhuriyar Benin.
“Lokacin da ake masa tambayoyi, ya amsa cewa kokon kan mutumin da aka gano nasa ne. Ya yi ikirarin cewa ya yi hijira ne daga Jamhuriyar Benin zuwa Najeriya kimanin shekaru hudu da suka gabata don yin sana’arsa, ba tare da wani takardar shige da fice ba, kuma shi likitane na gargajiya ne.”
Abiodun ya kuma ce wanda ake zargin ya kara da cewa ya yi tattaki zuwa jamhuriyar Benin kwanan nan, kuma a lokacin da ya shiga Najeriya ya ga wata jaka a hanya da kokon kai a cikinta.
“Shi (wanda ake zargin) ya ce ya daure shi ne a kan babur dinsa ya kai shi gida, saboda ya yi imanin cewa zai yi amfani da shi wajen aikinsa, kuma bai kai rahoto ga ‘yan sanda ba,” in ji kakakin ‘yan sandan jihar.
“Rundunar ‘yan sandan ta yaba da goyon bayan ‘yan Neja da sauran jama’a, kuma tana rokon su da kada su yi kasa a gwiwa ta hanyar sanar da ‘yan sanda idan suka ga wani bakon abu a cikin muhallinsu.”
Nan ba da jimawa ba za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotun.