Ƙauraye a Katsina sun Jikkata Mutane a Unguwannin Rahamawa, Abatuwa da Janbango

0

Bin Yaqoub Katsina @Katsina City News

 

Aƙalla kusan sati ɗaya kenan al’ummar yankin unguwannin Abatuwa, Rahamawa, Janbango da sauran unguwannin wannan rukunin, kullum hankalinsu a tashe ya ke, su na cikin fargaba sakamakon faɗace-faɗacen ƙauraye da ake ta yi a cikin unguwannin wanda abin ya yi muni sosai.

 

A cikin satinnan Kusan kullum da dare sai mutane na zaune su na fira ko hutawa a ƙofar gidajensu kawai sai dai su ga zugar (tawaga) ƙauraye ɗauke da gorori, wuƙake, adduna, da makamai masu muni daban-daban inda su ke dira kan mai-uwa-da-wabi (babu babba ba yaro, babu mata babu tsofi), an salwantar da dukiyoyi da lafiyar mutane daban-daban wasu ma rai hannun Allah yanzu haka.

 

A ranar Litinin 06/03/2023 wannan zugar ƙauraye sun shiga wannan unguwanni sun sari wani matashi a ƙafa mai suna Aliyu har ƙoƙon gwiwarsa ya fita, ƙarshe yanzu maganar cire ƙafar ake yi a Asibiti, sannan a ranar Talata 07/03/2023 har wayau sun ƙara dawowa sun yi ta’addancin kan mai Uwa da wabi inda su ka tadda shagon wani mai caji ana kiransa Bahago da ke yankin Filin Muntari, su ka lalata masa Kwamfuta da wayoyin mutane da su ka kawo caji. Abin bai tsaya nan ba sun daɓa wa wata yarinya mai soya awara wuƙa a ciki, (ita ma tana nan ta na jinya). Duk a  ranar, sun sari wani Abubakar a baya har ‘spinal cod’ ɗinsa ta samu matsala. Akwai wani da su ka yanka a wuya shima.

 

Shi kuwa wani mai suna Ibrahim Bello ya taso daga aikinsa zai koma gida, sun sare shi sosai a kansa da fuskarsa har hancinsa ya fita, yanzu haka ya na ta aman jini, ya na fafutikar lumfashi. Wani abin takaici iyalan wannan bawan Allah sun kai shi asibiti aka ce sai sun zo da jami’in tsaro, amma da su ka je wajan jami’an tsaron sai aka ce sai sun ba da wani ba’ali na kuɗi sannan a ɗauki bayanansu.

 

A asibitin ma su ka ce kuɗi sai Cash, wanda hakan bai samu ba sai da ƙyar alhali shi mara lafiyar na ta zubar da jini.

 

“Shin al’umma da me za su ji? a cikin unguwanninsu ma ba su huta ba, to ina za su sa kansu? Kuma masu ta’addancin nan ba su fi karfin a ɗaukar masu mataki ba amma an zura wa abin ido. Idan ma an ɗauki matakin to ana dira kan wanda babu ruwansa ne kamar yadda su ma ƙaurayen su ke dira kan wanda bai san hawa ba bai san sauka ba, mai makon abin ya tsaya iya su tunda su suka ji su ka gani. Wani abin tashin hankalin to duk waɗannan da aka lahanta wallahi babu ɗaya da ke dabanci ko wani abu mai kama da haka.” Inji wani Mazaunin Unguwar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here