Ƴan Sanda Sun Kama Gawurtaccen Ɗan Bindiga A Katsina

0

Daga Muhammad Kabir

Rundunar yan sanda a jahar katsina sunyi nasarar kama wani dan ta’adda mai suna Sulaiman Iliyasu, wanda ake ma lakabi da ‘Yar Bishiya, Mai Shekara Ashirin da takwas (28).

 

Da yake gabatar da mai laifin ga manema labarai, Mai Magana da yawun rundunar yan sanda ta jahar Katsina SP Gambo Isah yace, An kama wanda ake zargin ne da laifuka kala-kala, waɗanda suka shafi ta’addanci a jahar Katsina.

 

Gambo ya kara da cewa, wanda ake zargin ya shahara ya kware a ta’addanci. “Yana ƙarkashin ƙungiyar ƙasurgumin dan ta’adda wanda hukumar yan sanda ke nema ruwa a jallo, mai suna Dan Karami.

 

Dan ta’addan wanda ya addabi al’ummar yankin Jibia, Daddara, Sabuwa, Faskari, Kurfi, Dandume dama yankin Danmusa. Wanda ake zargin yace ya kashe mutane sama da goma sha biyar (15)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here