Kotu ta amince DSS su ci gaba da tsare Habu Tabule da Sheikh Isma’il Mangu

0

Kotu ta amince DSS su ci gaba da tsare Habu Tabule da Sheikh Isma’il Mangu har zuwa nan da kwana 7

 

Kotun Majistiri da ke No-man’s-land a Kano ƙarƙashin mai shari’a Aminu Gabari ta amince da roƙon hukumar DSS na ci gaba da tsare Jarumin Barkwancin nan Habu Tabule da kuma wani Malamin addini Sheikh Isma’il Ilyasu Mangu.

 

DSS sun nemi kotun ta basu damar ci gaba da tsare su domin faɗaɗa bincike kan zargin da ake musu na yin kalaman tunzuri da yunkurin tada tarzoma a zaɓen Kano da za a yi ranar Asabar.

 

Kotun ta sanya ranar 23 ga watan Maris da muke ciki inda za a dawo da su don ci gaba da shari’ar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here