‘Yan sanda sun kama wata mata dauke da kayan INEC na bogi

0

Rundunar ‘yan sanda a jihar Legas ta ce ta kama wata mata ‘yar shekaru 53 da haihuwa, wadda ake zargin an same ta da kayan zabe.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Benjamin Hundeyin, ne ya tabbatar da hakan ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ranar Juma’a.

Hundeyin ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar Alhamis da misalin karfe 4:00 na yamma. a Candos Road, Baruwa a unguwar Iyana-Ipaja a Legas.

Ya ce an kama wadda ake zargin ne a cikin wata cibiyar kasuwanci inda take yin kwafin.

“An kama ta da kayan INEC 550 daban-daban.

“An gano kwamfutar tafi-da-gidanka da ta yi amfani da ita wajen buga kayan kuma ba ta iya yin cikakken bayani kan yadda ta mallaki kayan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here