Dikko Umar Raɗɗa ya kaɗa ƙuri’arsa

0

Dan takarar gwamnan jihar Katsina a karkashin jam’iyyar APC, Dakta Dikko Umar Radda ya kaɗa ƙuri’arsa a rumfa mai lamba 010, Kofar Katika, kauyen Radda da misalin karfe 11 na safe

Da yake jawabi ga manema labarai jim kadan bayan kada kuri’ar, Raɗɗa ya bayyana kwarin gwiwar cewa mutanen jihar nagari, za su baiwa jam’iyyar APC gagarumin goyon baya a zaben gwamna da na ‘yan majalisar dokoki.

Raɗɗa yayi godiya ga Allah da ya sa zaben ya yiwu, ya kuma yabawa hukumar zaɓe ta INEC kan yadda ake gudanar da zaɓen ba tare da wata matsala ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here