Shugaban majalisar dokoki ta Legas ya lashe zabe karo na 6

0

An zabi shugaban majalisar dokokin jihar Legas, Mudashiru Obasa a karo na shida domin wakiltar mazabar Agege 1 a majalisar dokokin jihar.

 

Lukman Adeniji, jami’in zabe na INEC na zaben mazabar Agege ne ya bayyana hakan a yau Lahadi a cibiyar tattara sakamako da ke Orile Agege.

 

Ya ce jam’iyyun siyasa takwas ne su ka tsayar da ‘yan takara a zaben da aka gudanar a jiya Asabar.

 

A cewarsa, Mista Obasa ya samu kuri’u 17,214, inda ya doke Raheem Alani na jam’iyyar Labour wanda ya samu kuri’u 3,933, Kafayat Biobaku na ADC da kuri’u 62 sai kuma PDP mai kuri’u 1,609.

 

“Mudashiru Obasa na APC bayan ya cika sharuddan doka, ya samu kuri’u mafi yawa, sabo da haka an bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara kuma ya lashe zaben,” in ji Mista Adeniji.

 

A wani labarin kuma, Jubreel Abdulkareem, na jam’iyyar APC shi ma ya lashe kujerar majalisar wakilai ta mazabar Agege 2.

 

Mista Abdulkareem, wanda tsohon shugaban karamar hukumar Agege ne ya samu kuri’u 15,676 inda ya doke ‘yan takarar jam’iyyar Labour da PDP da suka samu kuri’u 7,159 da 1,598.

Daily Nigerian Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here