Wata gobarar ta kone shaguna a kasuwar Gamboru a Borno

0

An sake samun hadarin tashin gobara a kasuwar Gamboru da ke Jihar Borno.

Gobarar da ta tashi a jiya Asabar da karfe biyu na rana, tana ci gaba da ruruwa inda jami’an kashe gobara su ka isa domin shawo kan lamarin.

Da ya ke tabbatar da faruwar lamarin ga NAN a Maiduguri, kwamishinan ‘yan sandan jihar Borno, Abdu Umar, ya ce jami’an rundunar da sauran jami’an tsaro na fafatawa domin kashe gobarar.

Malam Umar ya ce an tura motocin kashe gobara kusan guda biyar zuwa wurin domin shawo kan lamarin.

NAN ta ruwaito cewa an ga daruruwan ’yan kasuwar da abin ya shafa suna ta fafutukar tattara ragowar kayayyakin su a cikin baraguzan ginin, yayin da wasu ke kallon yadda gobarar ke ci gaba da lalata wasu gine-ginen.

Daily Nigerian Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here