Magoya bayan jam’iyya mai mulki ta APC sun gudanar da zanga-zangar lumana bisa nuna kin amincewa da sakamakon zaɓe, wanda INEC ta sanar da Abba Kabir Yusuf na NNPP a matsayin Wada ya lashe zaben.
Abba Kabir Yusuf ne dai ya lashe zaɓen da ƙuri’u 1, 019, 602, inda ya doke babban abokin hamayyar sa, Dakta Nasiru Gawuna da ya samu ƙuri’u 890, 705.
Sai dai kuma jam’iyyar ta APC, a jiya Talata ta nuna rashin amince wa da sakamakon zaɓen, inda ta ce kamata yai INEC ta ayyana shi a matsayin wanda bai kammala ba.
Haka kuma sai jam’iyyar ta yanke hukuncin yin tattaki na lumana zuwa shelkwatar INEC ta jiha domin shigar da korafin ta na rashin amincewa da sakamakon zaɓen.
Daily Nigerian Hausa