Anyi Kira Da Masu Hannu Da Shuni Da Su Dinga Fitar Da Zakka A Kan Lokaci

0

Daga Muhammad Kabir

Ga banin karatuwar watan azumin Ramadana, Masu hannu da shuni suna raba kayayyakin masarufi ga al’ummar wasu kuma su bayar da Zakka daga cikin dukiyoyinsu.

 

Wannan kiran ya fito ne daga shugabar kamfanin Dadin Kowa Farm dake a garin Funtuwa, Hajiya Gimbiya Garba Ɗan’ammani.

 

Gimbiya tace da masu hannu da shuni na bayar da zakka kamar yadda Allah yace, da an fitar da mafiya yawan al’umma daga cikin kunci.

 

Zakka turba ce ta zaman lafiya, Duk wanda ke fitar da zakka kamar yadda Allah yace babu shi babu wasu fitin-tininu na duniya.

 

Gimbiya ta kara da cewa zakka sai Wanda Allah ya zaba Zai Iya fidda ta dai-dai. Da al’umma Zasu gane su fitar da Ita yadda Allah ya ce, da al’umma ta zauna lafiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here