Mutane ukku sun mutu, da dama suna kwance a asibiti sakamakon hatsarin mota a Katsina

0
KTSTA

Akalla fasinjoji uku ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin mota da ya afku a ‘Yar’ gamji, mai tazarar kilomita kadan daga babban birnin jihar Katsina, kan titin Katsina zuwa Dutsinma.

Jaridar Katsina Mirror ta ruwaito kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) reshen jihar Ibrahim Maiyaki Bazama, yace hatsarin ya rutsa da motar hukumar sufurin jihar Katsina (KTSTA) mota mai kirar Toyota Haice Bus wadda ta yi karo da wata motar bas Sharon Volkswagen. Da misalin karfe 8:30 na safiyar ranar Talata, inda Mutane ukku suka Mutu.

Ya kara da cewa tawagar ceto FRSC ta kwashe gawarwakin da wadanda suka samu raunuka daban-daban zuwa babban asibitin Katsina.

Kwamandan sashen na FRSC ya ce bas din KTSTA ta taho ne daga Katsina yayin da dayar motar ke kan hanyar zuwa birnin.

Da yake nuna alhinin hatsarin da ya faru, Bazama ya gargadi masu ababen hawa da su guji wuce gona da iri da kuma kiyaye duk ka’idojin tuki

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here