Akwai Bukatar A Sake Bibiyar Sakamakon Zaben Gwamnan Jihar Adamawa A Kananan Hukumomi 16 – Binani

0

‘Yar takarar gwamna jam’iyyar APC a jihar Adamawa, Sanata Aishatu Ahmed, wacce aka fi sani da Binani, ta bukaci a sake bibiyar sakamakon zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris a kananan hukumomi 16.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta yyana zaben gwamna a jihar ta Adamawa amatsayin wanda bai kammalu ba, tare da shirin sake gudanar da zaben a rumfunan zabe 69.

Har yanzu ba a tsayar da ranar ba.

Gwamna Ahmadu Fintiri da dan takarar PDP da kuma Binani na fafatawa amatsayin na gaba a an sakamakon zaben.

Binani ta ce lauyoyinta sun rubutawa INEC wasika domin ta sake bibiyar sakamakon zaben cikin kwanaki bakwai.

Ta yi ikirarin cewa zaben ya gamu da tashe-tashen hankula da magudi da kuma matsalar Na’urar BVAS.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here